Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa a karon farko Amurka ta gabatar masa da shawarar cewa Ukraine ta hakura ta mika wa Rasha wasu daga cikin yankunanta ciki har da Donbas, domin bude mata kofar shiga kungiyar tsaro ta NATO.
Zelensky ya ce wannan batun ya taso ne a yayin tattaunawar da ake yi kan kawo karshen yakin Ukraine da Rasha, sai dai ya jaddada cewa ba zai iya yanke hukunci shi kai kan yarjejeniya mai nauyi irin wannan ba, dole sai tare da amincewar al’ummar kasarsa.
Shugaban na Ukraine ya kuma kara da cewa Rasha ta yi watsi da shawarar dakatar da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi a yayin tattaunawar birnin Abu Dhabi bisa jagorancin Amurka.
A karshe Zelensky ya yi gargadin cewa yunkurin Rasha na sauya tsarin tsaro a Turai na iya haifar da sabbin rikice-rikice, yana mai cewa a mahangarsa, Tarayyar Turai da kungiyar NATO ne kadai ginshikan tsaron nahiyar.
Putin zai karbi bakwancin wakilan Amurka
A nata bangaren Rasha, na ci gaba da nuna adawa da fadada NATO zuwa gabashin Turai, inda shugaba Vladimir Putin ke ci gaba da jaddada adawa da bai Ukraine kujerar mamba a kungiyar. Haka kuma Rasha na neman NATO ta rage yawan dakarun da take jibgewa a kusa da iyakokinta, lamarin da kasashen yammacin Turai suka yi watsi da shi.
