Kasahen sun yi gargadin cewar hakan zai kara tsananta matsalar jin kai, da kuma kara jefa rayuwar mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su cikin hadari.

Baya ga  Spain,ministocin harkokin wajen Iceland,da Ireland, da  Luxemburg, da Malta, da Norwai, da Portugal da Slovenia suma, sun rattaba hannu kan wannan sanarwa.

Wannan sanarwa na zuwa ne, a daidai lokacin da firaministan Isra’ila  Benjamin Netanyahu  ke kare shirinsa a gaban manema labarai,

lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida, da suka hada da kawayensa masu ra’ayin rikau, da kuma  kasashen duniya.

Yanzu haka dai kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa  a kan shirin na Isra’ila na mamaye Gaza.

 

Share.

Comments are closed.